✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta sake sassauta dokar hana fita 

Wannan na zuwa ne bayan sanya dokar hana fita a ranar Alhamis da gwamnatin ta yi.

Gwamnatin Kano, ta sake sassauta lokacin hana fita daga 6 na safe zuwa 6 na yamma a jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Salman Dogo Garba ne, ya sanar da hakan bayan taron majalisar tsaron da aka yi a gidan gwamnatin jihar ranar Talata.

Ya ce hakan zai ba wa mazauna jihar damar ci gaba da gudanar al’amuransu na yau da kullum yayin da rundunar ke ci gaba da tabbatar da tsaro.

Dogo, ya buƙaci mazauna jihar da su rika komawa gidajensu kafin ƙarfe 6 na yamma, kuma za a sake duba dokar da zarar al’amura sun sake daidaita.

Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya roƙi Kanawa da su ci gaba da yin addu’o’i don samu zaman lafiya da ci gaba a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Gwamnatin jihar ta fara sassauta dokar hana fita ne daga 8 na safe zuwa 2 na rana a ranar Lahadi.

Aminiya ta ruwaito yadda tun asali gwamnatin ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 bayan da zanga-zangar lumana ta rikiɗe zuwa tarzoma a jihar.