✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta rufe ‘WellCare’ kan kin karbar tsoffin kudi

Gwamnatin Kano ta lashi takobin hukunta duk masu kin karbar tsoffin takardun Naira

Gwamnatin Jihar Kano ta ba da umarnin rufe shagon zamani na Wellcare nan take kan kin karbar tsoffin takardun Naira da aka sauya wa fasali daga hannun kwastomomi.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya umarci Shugaban Hukumar Kare Hakkin Masu Sayayya ta Jihar Kano, Baffa Dan’agundi, ya gaggauta rufe katafaren shagon da ke garin Kano ne a ranar Asabar.

Bayan rufe Wellcare, Dan’aguni ya ce gwamnatin jihar za ta dauki matakin shari’a a kan Wellcare, wanda abin da ya yi ya saba umarnin da gwamnatin ta bayar na ci gaba da amfani da tsoffin kudin a jihar.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ba ta haramta amfani da tsoffin takardun kudin ba, kuma duk  dan kasuwar da ta samu yana kin karbar su, zai yaba wa aya zabi.

Tuni kamfanin Wellcare Alliance Limited, suka aike da takardar neman afuwa ga Gwamna Gwanduje da kuma rokon ya ba da izinin sake bude shagon nasu da aka rufe.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Jihar Kano ta bi sahun jihohin da suka maka Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) a gaban Kotun Koli, sunan ta hana aiki da dokar haramta kashe tsoffin takardun kudin.

Idan ba a manta ba, Kotun Koli ta dage wa’adin haramta kashe tsoffin kudin daga ranar 10 ga watan Fabrairu da muke ciki, zuwa ranar 15 ga watan.

Aminiya ta kawo rahoton yadda Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ba da umarnin kama duk masu kin karbar tsoffin kudin.

A hannu guda kuma, duk da umarnin Kotun Koli, rahotanni sun nuna ’yan Najeriya na kin karbar tsoffin kudin.