Rahotanni daga Kano sun bayyana cewa wasu jami’an gwamnatin jihar tare da ’yan sanda sun rufe ofishin lauyan tsagin Shekarau a jam’iyyar APC na jihar, Mista Nureini Jimoh (SAN), da ke Lamba 16c kan titin Murtala Mohammed, a Jihar.
Idan ba a manta ba Mista Jimoh, shi ne lauyan da ya jagorancin nasarar tsagin Sanata Ibrahim Shekarau kan bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a shari’ar takaddamar shugabancin jam’iyyar APC a Jihar.
- Daliba da mahaifiyarta sun kawo ’yan daba su kai hari a makarantarsu
- Daukar kaya fiye da kima ne silar mutuwar ’yan Islamiyya a Bagwai —Ganduje
Lauyan ya tabbatar da rufe ginin da ofishin nasa ke ciki ga manema labarai.
Ya ce jami’an gwamnatin sun rufe shi a cikin ofishin tare da wasu ma’aikatansa da kuma wasu mutane.
Cikakken bayani na tafe…