✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kano ta mayar da gidan Dan Masani ‘gidan tarihi’

Gwamnati ta ce za ta yi haka ne saboda adana tarihi

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta sayi gidan marigayi Dan Masanin Kano, Ambasada Yusuf Maitama Sule, kuma za ta mayar da shi Cibiyar Bunkasa Dimokuradiyya da Shugabanci na gari da kuma gidan tarihi.

Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Laraba.

Ya kuma ce tuni aka fara aikin gine-gine a gidan marigayin, wanda kuma tsohon Jakadan Najeriya ne a Majalisar Dinkin Duniya, da kuma gidan Gwamnatin Birtaniya da aka fi sani da British Council da ke kan hanyar gidan Sarki a birnin Kano.

Kwamishinan ya kuma ce an ware Naira miliyan 621 domin aikin wanda aka kasa shi gida biyu, inda kashin farko zai fara da gidan tarihi da kuma na cibiyar, yayin da za a fara ginin da na gidan tarihin.

Malam Garba ya ce gwamnati ta yanke shawarar fara aikin ne domin ta adana tarihi saboda muhimmancinsu ga al’ada da tarihin mutanen jihar, domin amfanin ’yan gaba da kuma yawon bude ido.

Daga cikin abubuwan da ake sa ran cibiyar za ta rika gudanarwa sun hada da bayar da horo, adanawa da zamanantar da al’adun jihar Kano da kuma samar da hadin gwiwa da sauran cibiyoyin ilimi da ke ciki da wajen Najeriya a fannin bincike.