✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kano ta magantu kan zargin sayar da kotunan shari’ar Musulunci

Gwamnatin ta ce zarge-zargen sam ba su da tushe

Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan, ya ce gwamnatin jihar ba ta da niyyar sayar da wasu kotunan Shari’ar Musuluncin jihar sabanin yadda ake zargi.

Musa, wanda kuma shi ne Shugaban kwamitin sauya wa kadarorin gwamnati matsuguni na jihar, ne ya bayyana hakan a Kano ranar Laraba.

Wasu lauyoyin jihar – Sanusi Umar da Usman Imam da Bello Basi – ne suka garzaya gaban wata Babbar Kotun Jihar Kano suna neman ta hana gwamnatin yunkurin sayar da kotunan.

Kotunan da ake takaddama a kansu sun hada da Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gidan Maitatsine a ’Yan Awaki da ta ’Yan Alluna a Fagge da ta Shahuci da kuma ta Gwauron Dutse.

Sauran sun hada da ta Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kasuwar Kurmi da kuma ta Filin Hockey.

A cewar Kwamishinan, “Zargin da lauyoyin suke yi ba gaskiya ba ne, ba shi da tushe kuma yunkuri ne na bata sunan gwamnati.

“Gwamnati ba ta da niyyar sauya wa Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Gwauron Dutse da ta Filin Hockey da ke Hausawa.

“Batun sauya wa kotunan ’Yan Awaki waje shi ne saboda tashar mota da kasuwar Kofar Wambai ta mamaye harabar kotun.

“Bai kamata a ce kotun na fama da surutu da hayaniyar mutane da ta ababen hawa ba, saboda za su rika dauke hankalin kotun.

“Kotu tana bukatar waje mai cike da natsuwa. Kotun ’Yan Awaki kuma an mayar da ita sabuwar Jami’ar Bayero da ke Kano, inda ake da rukunin kotunan Shari’ar Musulunci da dama, wadanda ake kokarin kammalawa nan da karshen watan Satumban 2022,” inji shi. (NAN)

%d bloggers like this: