✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta lashe amanta kan hukunta masu kin karbar tsoffin kudi

Ba za mu iya hukunta kowa a kan hakan ba saboda ba ma son zaluntar kowane bangare.

Gwamnatin Jihar Kano ta lashe amanta dangane da barazanar da ta yi na daukar mataki kan duk masu kin karbar tsofaffin takardun kudi.

A sanarwar da ta fitar, Gwamnatin Kano ta ce a yanzu ba ta da damar ladabtar da wanda ya ki karbar tsoffin kudin.

Shugaban kwamitin ladabtar da masu kin karbar tsoffin takardun kudin, Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Dan Agundi ya bayyana cewa matakin da Babban Bankin Najeriya CBN ya dauka na daina karbar tsoffin kudin da kuma umarnin da ya bai wa bankunan kasuwanci na su yi koyi da shi, ya sanya suka janye wancan mataki.

“Kasancewar Gwamnatin Kano ta damu da kuncin da al’ummar jihar suka shiga sakamakon canjin kudin, ya sanya har ta fara rufe wasu wurare da ke kin karbar tsoffin kudin.

“Sai dai a yanzu bayan mun saurari bayanan Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya yi game d batun daina karbar kudin wanda ya ce ya fara aiki tun a ranar 10 ga watan Fabrairu.

“Haka kuma mun nemi bayanai daga bankuna sun sanar da mu cewa ba laifinsu ba ne da har suka nuna mana takardar umarnin da CBN ya ba su a kan hakan.

“A yanzu haka mun sanar da Gwamna cewa ba za mu iya hukunta kowa a kan hakan ba saboda ba mu son zaluntar kowane bangare na al’ummar Jihar Kano da kuma na ’yan kasuwa.”

Dan Agundi ya ce a halin yanzu dai za su ci gaba da kasa kunne domin sauraron hukuncin da Kotun Koli za ta dauka kan wannan mataki a gaba.