Hukumar Kare Masu Sayen Kayayyaki ta Jihar Kano ta kama jabun magunguna na kimanin Naira miliyan 300 a daren ranar Talata.
Mukaddashin shugaban hukumar, Baffa Babba Dan Agundi ya ce wani dan kishin jihar ne ya fallasa wani mutum da ke hada jabun magungunan a kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi (Sabon Gari) a birnin Kano.
- Gaskiyar nada Sarkin Kano Sanusi II Khalifan Tijjaniyah
- An cafke masu safarar mutane a Katsina
- An dawo da ‘yan Najeriya 160 da suka makale a Libya
- Gaskiyar nada Sarkin Kano Sanusi II Khalifan Tijjaniyah
Dan Agundi, wanda ya samu wakilcin mai bai wa Gwamnan Kano shawara kan KAROTA Nasiru Usman Na’ibawa, ya ce jami’an sun isa kasuwar da misalin karfe 9:30 na daren Talata, bayan samun labarin.
Ya kara da cewa kwamitin ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen fataucin jabun magunguna a jihar.
Na’ibawa, ya yaba wa jama’ar jihar kan yadda suke ba wa kwamitin hadin kai da bayanan abubuwan da ke faruwa a lunguna da sako.
Kazalika, ya roki jama’ar da su ci gaba da ba da bayanan da suka dace don dakile yaduwar laifuka da suka shafi fataucin miyagun kwayoyi.