✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta janye dokar hana fita

Gwamnatin ta ce ta dage dokar ne bayan ta yi nazari da kuma yadda aka samu wanzuwar kwanciyar hankali

Gwamantin Jihar Kano ta da janye dokar hana zirga-zirga da ta sanya a safiyar Litinin bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar da nufin ’yan majalisar jihar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin da dare, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Muhammad Garba, ya ce gwamnatin ta dage dokar ne bayan ta yi nazari kan lamarin da kuma yadda aka samu wanzuwar kwanciyar hankali a fadin jihar.

Kwamishinan ya yi kira ga bankunan kasuwanci da ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar da su fito su ci gaba da sana’o’insu na yau da kullum.

Ya bayyana cewa da farko an sanya dokar ce da nufin tabbtar da tsaro.

A safiyar Litinin da aka sanya dokar ce Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar da cewa Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya ci zaben gwamnan Jihar.

Sai dai duk da dokar, mutane sun yi gudanar shagulgulan murnar cin zaben.

Sai dai a wasu wuraren an samu rahotannin farfasa wuraren yakin neman zaben jam’iyyar APC mai mulki da ta fadi zaben.

A safiyar ranar kuma wasu bata gari suka cinna wa gidan mawakin siyasa na jam’iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara, wuta, amma jami’an tsaro suka cafke su, aka kuma kashe wutar.

Shi ma wani fitaccen mawaki Baban Chinedu, ya bayyana wa kafar yada labarai ta DW cewa an kai kwatankwacin harin a ofishinsa na daukar sauti, inda aka caka wa wani kaninsa wuka, aka kwashe kayan aikin da ke cikin wurin.

Ya ce wasu makwabtansa sun tsaya kai da fata sun hada lalata dukiyarsa a wani hari da bata-gari suka yi yunkurin kaiwa wani gidan da yake adana kayan aikinsa.

Hare-haren dai sun samu Allah wadai daga jama’a.