✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Sarauta: Gwamnatin Kano ta haramta zanga-zanga

Gwamna Abba ya ba da umarnin tsare duk wanda aka kama yana gudanar da zanga-zanga a fadin jihar Kano

Gwamnatin Kano ta haramta yin zanga-zanga ko taruwar jama’a da nufin haka a fadin jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci jami’an tsaro su tsare duk masu yunkurin gudanar da zanga-zanga ko tayar da zaune tsaye a fadin jihar.

Sanarwar da ya fito daga kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa a ranar Laraba ta kara da cewa gwamnan ya dauki matakin ne domin tabbatar da doka da oda.

“Mun samu rahoto cewa wasu fitattun ’yan jam’iyyar adawa na shirin daukar nauyin zanga-zangat dalibai da ’yan siyasa domin goyon bayan tubabben Sarkin Kano Aminu Ado Bayero.

“Saboda haka muke gargadin dalibai da sauran mutane cewa kada su bari miyagun mutane su yi wasa da hankalinsu wajen tayar da fitina a Kano.”

A karshe ya bukaci Kamawa da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin bin doka ba tare da wata fargaba ba.

Gwamnati kuma za ta ci gaba da yin abin da ya dace wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.