Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da sanarwar sanya dokar haramta shan sigari a bainar jama’a a duk fadin jihar.
Haramcin ya biyo bayan kiyasin da aka yi a kwanakin baya cewa akwai mutum fiye da dubu 16 da ke mutuwa duk shekara sakamakon zukar hayakin sigari a Najeriya.
Gwamnatin ta bayyana haka ne ta bakin Kwamishinan Kiwon Lafiya na Jihar, Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa a yayin taron manema labarai a daidai lokacin da ake bikin Ranar Hana Shan Sigari ta Duniya.
Dokta Tsanyawa ya ce Gwamnatin Jihar tana aiki tukuru wajen ganin ta rage yawan masu shan sigari gaba daya a Jihar.
“Muna da dokar hana shan taba a cikin jama’a da sayarwa yara ‘yan kasa da shekara 18,” inji shi.
Ya kara da cewa gwamnatin za ta himmatu wajen wayar wa al’umma kai su fahimci hadarin da ke tattare da zukar hayakin taba da dalilin da ya sa ya kamata su daina shan tabar.
A cewarsa, gwamnatin ta mayar da hankali sosai tare da kashe makudan kudade wajen yaki da cututtukan da ba a daukar su da suka hada da cutar hawan jini da asma da ciwon huhu da kansa da sauransu.
Kwamishinan ya kara da cewa zuwa yanzu akwai doka a gaban Zauren Majalisar Jihar a kan kafa hukumar da za ta kula da hana shan miyagun kwayoyi wanda ake son kafawa da zimmar rage harkar shaye-shaye a tsakanin al’ummar jihar.
A daya gefen kuma, Shugaban Kungiyar Farar Hula ta CISLAC mai rajin inganta ayyukan Majalisun Dokoki a Najeriya, Kwamred Auwal Musa Rafsanjani, ya ce alkaluma sun nuni da cewa akwai mutum biliyan 1.3 da ke ta’ammali da tabar sigari a duniya.
Kazalika, alkaluman sun tabbatar da cewa ana cinikin karan sigari biliyan 18 duk shekara a Najeriya.