Gwamnatin Jihar Kano ta yaba wa kwamitin dake samar da abincin buda baki na Ramadan kan yadda yake raba abinci ga mabukata a fadin jihar.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya yi wannan yabon a ranar Talata yayin da yake rangadin duba yadda aikin raba abincin buda bakin ke gudana a Karamar Hukumar Nassarawa.
- Gobara ta lakume ofishin INEC a Kano
- Direba da karen mota sun yi wa mai cutar HIV fyade
- Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Walter Mondale ya mutu
Garba, wanda shi ne ke jagorantar kwamatin da Gwamnatin Jihar ta kafa ya ce tsarin rabon ya yi daidai da ka’idojin da masana suka gindaya na kariyar cutar COVID-19.
Kwamishinan ya bukaci masu amfana da rabon abincin da su kiyaye da ka’idojin da masana kiwon lafiya suka shimfida na kariya daga cutar COVID-19.
Garba, ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni dake jihar da suma su bayar da tasu gudunmawar wajen ciyar da mabukata a wannan watan, ta yadda ciyarwar zata karade dukkan lungu da sakon jihar.
Kwamishinan ya ce gwamnatin Ganduje ta kirkiro shirin ne da nufin tallafawa marasa karfi da abincin a watan Azumin Ramadan.
Ciyarwar ta Azumin bana dai an fadada ta zuwa ilahirin Kananan Hukumomi jihar 44.