Gwamna Abdullahi Ganduje ya bude gidajen kallon kwallon kafa a fadin jihar Kano, yayin da ke shirin komawa gasannin kwallon kafa a nahiyar Turai.
Gwamnan ya kuma ya bukaci gidajen kallon da su kiyaye matakan kariya daga kamuwa da cutar coronavirus.
Ya kuma wajabta amfani da takunkumi da wanke hannu da kuma bayar da tazara da sauransu a gidajen kallon.
“Sakamakon matakinmu na sake farfado da tattalin arzikinmu ta hanyar bude harkokin kasuwanci, na bayar da umurnin bude dukkan gidajen kallo daga yau din nan”, inji gwamnan.
- Za a fara aikin titin jirgin kasan Kano-Legas a watan Agusta
- ‘Coronavirus ta kashe mutum 587 a Kano cikin mako biyar’
- Masu coronavirus a Kano sun haura 1,000
Ganduje ya kuma ba da tallafin takunkumi guda 40,000 a raba wa gidajen kallo domin ba su kwarin gwiwa kiyaye matakan kariya.
Hakan ta faru ne bayan gwamnan ya karbi bakuncin Kungiyar Gidajen Kallon Kwallo ta Jihar a ofishinsa.
Shugaban kungiyar Sharu Rabi’u Ahlan ya yaba da matakan da gwamnatin jihar Kano ta dauka na dakile cutar.
Sharu Rabi’u ya kuma ba da tabbacin za su kiyaye dokokin dakile cutar ta coronavirus idan suka koma aiki.
Kawo yanzu gwamnatin jihar ta bude galibin wuraren taruwar jama’a, banda makarantu da zaurukan gudanar da bukukuwa, a kwanaki ukun da aka jingine dokar hana fita a jihar.