Gwamnatin Jihar Kano ta bai wa wani karamin ma’aikaci kujerar aikin Hajji da takardar daukar aiki ta dindindin da kyautar Naira miliyan daya, saboda mayar da kudin guzurin alhazan wata karamar hukuma ce da ya tsinta a harabar Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar.
Gwamnan Jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a yayin da yake karbar rahoton hukumar game da aikin Hajjin bana.
- Falasɗinawa miliyan ɗaya na rige-rigen ficewa daga Zirin Gaza
- MDD ta zaɓi kasashen Afirka 4 a Kwamitin Kare Hakkin Bil Adama na Duniya
Mutumin mai suna Dayyabu Bala Gezawa (wanda aka fi sani da Dan Gezawa) bayan ya tsinci kudin ya mayar da su ga Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa.
Gwamnan ya ce, “Don haka muka ga dacewar mu kyautata wa wannan ma’aikaci, saboda gaskiya da halin kwarai da ya nuna, duk da kasancewarsa karamin ma’aikaci da kuma da ake ciki na matsin tattalin arziki a kasar nan.”
Gwamnatin ta sha alwashin ci gaba da daukar nauyin maganin wani daga cikin alhazanta da yake kwance a yanzu haka a wani asibiti da ke birnin Makka.
Mahajjacin mai suna Abdullahi Muhammad ya kamu da rashin lafiya ne bayan kammala aikin Hajji, inda likitoci suka bayar da shawarar ya ci gaba da zama a hannunsu zuwa wani lokaci.
Gwamnan ya ce, gwamnatin za ta dauki nauyin tura iyalin marar lafiyar don ba shi kulawa a can inda yake jinya.
Har ila yau, gwamnatin ta lashi takobin ci gaba da bai wa Hukumar Jin Dadin Alhazan duk kulawar da take bukata don gudanar da aikin cikin nasara.
A jawabin Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bayyana cewa, duk da cewa sun karbi aikin gudanar da jigilar a kurarren lokaci, amma sun yi nasarar gudanar da aikin Hajjin cikin nasara, inda ba a bar maniyyaci ko guda daya a kasa ba.
Ya ce, “Kamar yadda kowa ya sani, mun karbi gwamnati ana gab da fara gudanar da aikin Hajji, ga shi kuma gwamnatin baya ta yi wa-kaci-wa-tashi da aikin, amma da taimakon Mai girma Gwamna, wanda ya ba mu hadin kai dari bisa dari, mun yi kokari, inda muka yi nasarar aikinmu.”
Danbappa ya nemi gwamnatin ta sahale wa hukumar fara shirye-shiryen aikin Hajjn badi a kan lokaci don gudanar da aikin cikin nasara.
Taron ya samu wakilcin masu ruwa-da-tsaki da suka hada da shugabannin aikin Hajji na kananan hukumomi 44 da malaman bita da malaman lafiya da sauransu.