Gwamnatin Jihar Kano, ta ɗauki malamai 5,000 aiki domin farfaɗo da fannin ilimi a faɗin jihar.
Gwamna Abba Yusuf ne, ya bayyana hakan ne yayin da yake ayyana dokar ta baci kan ilimi a ranar Asabar a Kano.
- Maƙiyan Kano sun hana Abba aiki tsawon shekara guda — Kwankwaso
- Fitattun waƙoƙin siyasa da suka yi tasiri a wannan jamhuriyya
Ya jaddada buƙatar samar da ingantattun malamai don yin aiki a makarantun gwamnati da ke jihar.
Yusuf, ya ce shirin na da nufin samar da abubuwan da makarantun gwamnati a jihar ke buƙata don inganta ilimi a jihar.
Gwamnan ya ce zamanin da ɗalibai za su ke karatu cikin mawuyacin hali ya ƙare.
“Sanar da dokar ta-baci a fannin ilimi wani mataki ne mai ƙarfi na tunkarar ƙalubalen da wannan fanni ke fuskata.
“Alƙawarin gwamnati na samar da kayan koyo da ababen more rayuwa da za su taimaka sosai wajen inganta ilimi a jihar na ,” in ji shi.
“Sama da ɗalibai miliyan 4.7 ke zama a ƙasa domin ɗaukar darasi, yayin da makarantu 400 ne kaɗai ke da malamin kowane darasi,” in ji shi.
Yusuf ya ce gwamnatin da ta shuɗe ta rufe makarantu yayin da waɗanda suka lalace ta cefanar da su.
“Malamai suna kokawa kam rashin kayan aiki na zamani,” in ji shi.
Ya yi alƙawarin magance matsalolin dabaibaye ɓangaren ilimin a jihar gaba ɗaya.
Wannan ya haɗa da ƙarancin ƙwararrun malamai, rashin isassun kayan aiki da sauransu.