✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta ƙi amincewa da hana hawan sallah a jihar

Gwamnatin ta ce Kwamishinan 'yan sandan jihar na wuce gona da iri.

Gwamnatin Jihar Kano ta soki rundunar ’yan sandan jihar kan watsi da umarnin gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, game da bikin hawan sallah a jihar.

A wani taron manema labarai, babban lauyan jihar, Haruna Isah Dederi, ya yi tambaya kan dalilin da ya sa Kwamishinan ’yan sandan jihar ya hana gudanar da bukukuwan hawan sallah babba ba tare da tuntubar gwamnan jihar ba.

Ya jaddada cewa gwamna shi ne babban jami’in tsaro don haka ya kamata a ce shi ne zai yanke irin wannan hukunci.

Dederi ya ce, “Ta yaya wani zai hana bukukuwan Sallah a Kano, bai kamata Gwamna ya ga wannan mataki a kafafen sada zumunta ba, wane ne ke bai wa Kwamishinan ’yan sanda ƙwarin gwiwa kan wuce gona da iri, yana fakewa da karɓar umarni daga sama. Me mutanen Kano suka yi da suka cancanci hakan?

Dangane da hukuncin da kotu ta yanke kan take haƙƙin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, Dederi ya bayyana cewa gwamnati ba ta take haƙƙin Sarkin ba.

Ya bayyana cewa Sarkin ya zauna a ƙaramar fadar Nassarawa ne don gashin kansa, babu wanda ya tsare shi.

“Haƙƙin Gwamna ne ya kare jihar, lokacin da tsohon Sarki ya zo da ɓata-gari yana neman jefa jiha cikin tashin hankali, Gwamna ya bayar da umarnin kama shi, duk da haka babu jami’an tsaron da suka kama shi kuma ya ci gaba da gudanar da al’amura kafafen sada zumunta.”

Aminiya ta ruwaito cewar rundunar ‘yan sandan jihar ta haramta hawan sallah a bana.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunar ta ɗauki matakin ne domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da tsaro a jihar.

Wannan dai na zuwa ne bayan da ake ci gaba da dambaruwa kan masarautar Kano, duk da cewar babbar kotun tarayya da ke jihar, ta umarci gwamnatin Kano ta biya Aminu Ado Bayero tarar miliyan 10 kan danne masa haƙƙinsa.