Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake maka jagoran mabiya Shi’a na Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky a gaban Babbar Kotun Tarayya bisa zargin cin amanar kasa.
Hakan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan Babbar Kotun Jihar Kaduna ta saki malamin da matarsa, Zeenat.
Aminiya ta rawaito cewa a ranar Laraba kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Gideon Kurada ta ce bai kamata tun farko ma Gwamnatin Jihar Kaduna ta shigar da karar ba saboda ba ta da hurumin tuhumar wani kan abin da a lokacin ba laifi ba ne.
Alkalin ya ce tuhumar da aka yi wa El-Zakzaky da matarsa a 2018, dogaro da dokokin Kundin Penal Code na Jihar na 2017 kan laifin da ake zargin an aikata a 2015 ba zai zama abin dogaro ba.
To sai dai gwamnatin ta ce bata gamsu da hukuncin da alkalin ya zartar ba.
Babban Mai Shigar da Kara na Gwamnatin Jihar, Dari Bayero ya ce babu makawa za su daukaka karar.
A cewarsa, “Tabbas za mu daukaka kara, wannan ko shakka babu a kai. Tuni ma mun karbi kwafin hukuncin kotun, saboda muna da tantama a kan shi, la’akari da hujjojin da suke a kasa.”
An garzaya da El-Zakzaky Abuja
Aminiya ta gano cewa jagoran na ’yan Shi’a da matarsa tuni suka tafi Birnin Tarayya, Abuja, domin ganin likita.
Yunkurin malamin na barin Jihar Kaduna a ranar Laraba dai ya gamu da cikas bayan da aka shaida masa cewa an rufe filin jirgi a lokacin da ya isa domin tashi, kamar yadda wata majiya ta tabbatar mana.
El-Zakzaky tare da matarsa da rakiyar ’yan uwa da abokan arziki daga bisani sun isa filin jirgin sama na Kaduna da misalin karfe 8:30 na safiya Alhamis inda suka dauki shatar jirgi zuwa Abuja.