✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta horar da matasa 1,470 kan sana’o’i

Gwamna Umaru Tanko Almakura na Jihar Nasarawa ya bayyana kudurin gwamnatinsa wajen himmatuwa sosai wajen koyar da sana’o’i da karsasa matasan jihar ta yadda tattalin…

Gwamna Umaru Tanko Almakura na Jihar Nasarawa ya bayyana kudurin gwamnatinsa wajen himmatuwa sosai wajen koyar da sana’o’i da karsasa matasan jihar ta yadda tattalin arziki zai bunkasa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a bikin yaye matasa dubu da dari hudu da saba’in (1,470) da aka horar a karkashin kashi na farko na shirin karfafa matasan jihar wanda aka yi wa lakabin “NAYES” a Turance.
An gudanar bikin ne kuwa a sansanin ’yan yi wa kasa hidima na Magaji danyamusa da ke Kaffi, inda ya nuna cewa shirin, zai samar wa matasan jihar aikin yi, zai kuma rage zaman kashe wando a tsakaninsu, lamarin da yake daya daga cikin muhimman manufofin gwamnatinsa.
Ya ce gwamnatinsa ta sayo kayyakin aiki na kimanin Naira miliyan 300 da za a raba wa cibiyoyin koyon sana’o’in hannu a fadin jihar nan ba da jimawa ba.
Ana sa ran matasan da aka horar, za su yi aiki ne a matsayin masu sa ido a kan batun tsaro da taimakawa wajen saisaita masu ababen hawa a kan hanya da kuma tsabtace muhalli da sauran ayyukan da suka dace.
Gwamnan ya bukaci wadanda aka horar su yi kyakkyawan amfani da horo da suka samu domin amfanar al’ummar jihar da ma kasa baki daya. Daga nan ya yi kira ga al’ummar jihar baki daya su cigaba da tabbatar da dorewar zaman lafiyar da ke dawo wa jihar, musamman kasancewar zaben kananan hukumomi yana karatowa.
A jawabansu daban-daban, shugaban kwamitin aiwatar da shirin horar da matasan, Mista Daniel Oga Ogasi da Mataimakin gwamna na musamman a kan harkokin karfafa matasan jihar, Alhaji Murtala Adogi da kuma jami’in horar da matasan, Malam Shehu Yahu Mai ritaya duk sun yaba wa Gwamna Almakura ne dangane da kirkiro da shirin, wanda suka bayyana mahimmancinsa ga matasan. Sun kuma bukaci matasan su tabbatar sun yi kyakkyawan amfani da horon da suka samu don cigaban jihar baki daya.