✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Jihar Gombe ta kuduri yakar yunwa

Gwamnatin Jihar Gombe ta hada kai da Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Majalisar dinkin Duniya Majalisar (UNFPA) wajen ba da kasonta na Naira miliyan…

Gwamnatin Jihar Gombe ta hada kai da Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Majalisar dinkin Duniya Majalisar (UNFPA) wajen ba da kasonta na Naira miliyan 120 domin yaki da  yunwa da rashin abinci mai gina jiki ga kananan yara  a jihar.
Kwamishinan Tsare-Tsare da Tattalin Arziki na Jihar Gombe ne, Alhaji danladi Muhammad Pantami ya bayyana haka a lokacin wani taro na masu ruwa-da-tsaki kan shirin Majalisar dinkin Duniya da ya gudana a Gombe.
Kwamishinan ya ce ba ya ga wannan, gwamnatin ta shiga wata yarjejeniya da Hukumar UNFPA, inda ta ba da kimanin Naira miliyan 200 daga kasafin kudi na bana domin taimaka wa wannan shiri a matsayin gudunmawarta ga shirin.
Ya yi amfani da wannan dama inda ya gode wa kungiyar Tarayyar Turai, kan adda take ba da gudunmawa wajen ganin an taimaka wa bangaren kula da lafiya a fadin jihar.
Ya ce a shirye-shiryen da ake yi na shiga wani sabon shiri na UNDAF 4, yana fata shirin zai ci gaba don ganin an magance matsalolin da suka dabaibaye jihar, sannan ya ce gwamnati za ta ci gaba da ba da tata gudunmawar don ganin an yaukaka dankon zumuncin.
Da take jawabi a lokacin taron, babbar jami’ar hukumar a Najeriya, Ratidzai Ndhlou, wacce Hajiya Bahijjatu Bello Garko ta wakilta, cewa ta yi kungiyar Tarayyar Turai, ta karfafa al’amuranta ne wajen ganin ta ciyar da kungiyoyin mata da matasa gaba da harkar karatu da kungiyoyin fararen hula da sauransu.
Ta ce yanzu haka suna gudanar da wannan taro a yankuna shida na Najeriya kuma Jihar Gombe tana daga ciki saboda kyakkyawar alakarta da kungiyar Tarayyar Turai.
Hajiya Bahijjatu ta ce sun hadu a Gombe ne domin tattaunawa a gano matsalolin da ba su cikin  matsalolin da kungiyar ta zayyana don mayar da hankali a kansu, inda bayan kammala taron zai sa Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su samu cikakken bayani kan shirin na UNDAF.