Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya dokar hana fita na awa 24 a garin Billiri inda rikicin nadin Sarautar Mai Tangale ta ki ci, ta ki karewa.
Sanya dokar na zuwa ne bayan zanga-zangar da mata da kananan yara ke yi wadda taa kai ga kone Wani masallaci da wasu gidaje a garin ranar jumaa
Rikicin nada sabon Mai Tangale na 16 da ya sa mata da kananan yara tare kan babbar hanyar Gombe zuwa Yola ta kai ga kona wani masallaci da wasu gidaje a garin.
Biyo bayan hakan tasa gwamnatin jihar Gombe ta sanya dokar hana fita na tsawon sa’a 24 a Karamar Hukumar Billiri da kewaye inda dokar ta fara aiki nan take daga yau Juma’a.
Da yake sanar wa manema labarai, Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya ce sanya dokar ne abu mafi dacewa dan shawo kan zanga-zangar da aka fara kwana uku da suka wuce a garin na Billiri.
Farfesa Njodi, ya ce zanga-zangar ta biyo bayan wata jita-jita da wasu ke yadawa cewa an nada sabon Mai Tangale wanda kuma ba hakan ba ne.
Ya ce su dai sun kawo zabin su mutum uku sun mika wa gwamnati, kuma kamata ya yi su jira sanarwar wanda gwamnati za ta nada amma sai ba su yi ba suka fita zanga-zanga na tare hanya.
A cewarsa ida sarki ya mutu masu nada sarki suka kawo wadanda suke so a zaba a ciki, dokar kasa ta bai wa gwamna dama na yada wanda yake so.
Idan ma a cikin su babu wanda gwamnati ta ga ya dace za ta iya nemo wani daga waje ta nada ya zama sarki.