Gwamnatin Jihar Gombe ta rufe dukkan makarantun koyar da aikin jinya masu zaman kansu da ke fadin Jihar su fiye da 10.
Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Habu Dahiru ne ya sanar da hakan a lokacin hirar sa da manema labarai a yau laraba Jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta Jihar.
- Ministan Buhari ya ajiye mukaminsa saboda takarar Shugaban Kasa
- Yadda wahalar nan fetur ke shafar rayuwar mazauna Abuja
Ya ce rufe makarantun ya biyo bayan rashin bin ka’idojin da aka bude su, kuma ba su da gine-gine da dakunan gwaje-gwaje da kwararrun malamai.
A cewar Kwamishinan, hakan ne ya sa ko daliban sun kammala karatun a makarantun ba sa iya samun aiki.
Kwamishinan ya kara da cewa daliban basa samun takardar kammala karatu mai inganci wanda hakan yasa a mafi yawan makarantun ake yaye dalibai marasa kwarewa.
Ya ce masu makarantun suna zuwa Hukumar yi wa Kamfanoni Rajista (CAC) ana yi musu rijista duk da cewa ba hurumin su ba ne.
“rin daliban da ake yayewa sune suke bin kasuwannin kauyuka suna yi wa mutane allura da karin ruwa sakamakon rashin kwarewa wanda yin hakan kuskure ne,” inji shi.
Dokta Habu Dahiru ya ce kwamitin da gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya ta kafa zai zaga dukkan makarantun dan gane wa idonsa ire-iren wadannan makarantun dan ganin wadanda suka cika ka’ida an bar su, wadanda ba su cika ba kuma a kulle su.
“Kawai sai wani ya je ya ari makarantar firamare ya dinga karatu a ranakun Asabar da Lahadi ba dakin gwaje-gwaje ba littattafai,” inji Kwamishinan.