✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Gombe ta nada sabon Mai Tangale

An nada Malam Danladi Sanusi Maiyamba a matsayin sabon Mai Tangale kwanaki bayan tarzoma kan nadin.

Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya sanar da nada Malam Danladi Sanusi Maiyamba a matsayin sabon Mai Tangale.

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautun Jihar Gombe, Ibrahim Dasuki Jalo ya ce gwamnan ya nada sabon Mai Tangale bayan Masu Zabar Sarkin Masarautar sun gabatar masa da zabin da suka yi.

Da yek gabatar wa sabon Mai Tangalen takardar nadin nasa a Poshiya, Billiri, ya ce an nada shi ne bisa la’akari da dacewarsa da kuma nagartarsa.

Sanarwar hakan da Darakta-Janar na Yada Labaran Gidan Gwamnatin Jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ya fitar ta ce gwamnan Masu Zabar Sarki tara daga Masarautar Billiri da wasu sarakuna da manyan jami’an gwamnati na da naga cikin mahalarta mika takardar nadin ga sabon Mai Tangalen.

Sanarwar ta ne nan gaba za a gudanar da bikin nadin da muka mika masa sandar mulki.

Tun da farko takaddama kan nadin sabon Mai Tangale bayan rasuwar Mai Tangle na 16, Abdu Buba Mai Sheru III.

Wasu ’yan kabilar ta Tangale sun yi tarzoma a garin Billiri bayan bazuwar jita-jitan cewa Gwamnan ya nada wanda jama’ar Masarautar ba sa so.

Tarzomar masu boyen da suka tare hanyar Gombe zuwa Yola tare da kone-konen gidaje da masallaci ya kai ga Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya dokar hana fita a garin Billiri.