Gwamnatin Jihar Filato ta kafa kotuna bakwai don hukumta mutum 307 da ake tuhuma da fasa rumbunan abincin tallafin COVID-19 a wurare daban-daban na jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Danladi Atu ne ya bayyana haka, a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a gidan gwamnatin jihar a ranar Litinin, bayan kammala taron gaggawa da majalisar tsaron jihar ta kira kan yadda aka yi kwanaki biyu bata-gari na fasa rumbunan da aka ajiye abincin COVID-19 da kuma bata kadarorin gwamnatin jihar.
- Gwamnatin Filato za ta hukunta wadanda suka fasa rumbunan ajiye abinci
- Ganduje zai gabatar da kasafin kudi a majalisa ranar Talata
- Batanci ga Annabi: An dage zaman kotu saboda rashin lauya
Ya ce jami’an tsaro na farautar wadanda suka fasa rumbunan abincin da aka sace, don ganin an hukumta su, tare da dawo da kayayyakin abincin da aka sace.
Ya ce ya zuwa yanzu hankula sun fara kwanciya a jihar, amma duk da haka akwai barazanar bata-garin, da ke iya kai wa wasu kadarorin gwamnati da wuraren kasuwanci masu zaman kansu hari.
Ya ce an umarci jami’an tsaro su kara tsurara bincike a dukkan shingayensu Kananan Hukumomin Jos ta Arewa da ta Kudu, don tabbatar da dokar hana fita da aka kafa.
Sakataren gwamnatin ya gargadi al’ummar jihar su guji amfani da kayan abincin da aka sato saboda suna dauke da gubar maganin da zai iya cutar da duk wanda ya yi amfani da su.