Gwamnatin Jihar Filato, ta janye dokar hana tuka Keke NAPEP a garin Jos da kewaye tare da sassauta dokar hana zirga-zirga, a Karamar Hukumar Jos ta Arewa.
Gwamnan Jihar, Simon Lalong, ya amince da hakan ne bayan kammala taron Majalisar Tsaron Jihar, da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.
- Jami’in gwamnati ‘ya kashe kansa’ bayan EFCC ta gayyace shi
- Yadda datse sadarwa ta shafi kasuwanci a Zamfara
Wata sanarwa da aka fitar, mai dauke da san hanun Daraktan Watsa Labaran gwamnan, Dokta Makut Macham, ce ta bayyana haka.
Sanarwar ta yi bayanin cewa gwamnatin ta amince ta janye dokar hana tuka Keke NAPEP daga ranar Talata.
Dokar hana zirga-zirga kuma ta dawo daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na yamma, maimakon daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe, wadda itama ta fara aiki, daga ranar Talata.
Sai dai ta bayyana cewa dokar haramta Keke NAPEP daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe tana nan; don haka babu maganar amfani da su daga karfe 6 na yamma zuwa karfe 6 na safe, a garin Jos da kewaye.