✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin dakingari ta kamu da cutar Ebola – Sani Dodo

Alhaji Sani Dodo na hannun daman Gwamna Sa’idu dakingari ne daga shekara 2010 zuwa 2014, amma yanzu sun yi hannun riga, ya koma Jam’iyyar APC,…

Alhaji Sani DodoAlhaji Sani Dodo na hannun daman Gwamna Sa’idu dakingari ne daga shekara 2010 zuwa 2014, amma yanzu sun yi hannun riga, ya koma Jam’iyyar APC, inda aka zabe shi kakakin jam’iyyar a jihar.  A zantawansa da wakilinmu ya yi fashin baki kan rikatar-rikatar da gwamnatin dakingari ke fuskanta:

Aminiya: Ana rade-radin cewa sabon shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi dan kwangilar Jam’iyyar PDP ne, mene ne gaskiyar lamarin?
Sani Dodo: A matsayina na kakakin Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi, ba ni da masaniya game da wannan labari, kuma kowa ya san shugaban jam’iyyarmu Lauya Attahiru Maccido ba ya da wata alaka da PDP. Duk lokacin da mutum ya fito takara ba a rasa masu yi masa kazafi da batanci, kuma za mu ci gaba da gwagwarmaya har sai mun kifar da gwamnatin PDP a zabe mai zuwa tun daga kan kansila har zuwa Shugaban kasa da yardar Allah.
Aminiya: Me za ka ce game da masu cewa Sanata Atiku Bagudu ya koma APC ne domin Gwamna dakingari ba zai goya masa baya a PDP ba?
Sani Dodo: Sanata Atiku Bagudu dan PDP ne ba shi da alaka da jam’iyyarmu ta APC, amma duk da haka Jam’iyyar APC ta kowa da kowa ce ba mu da gefe, kuma shigowar irin su Atiku Bagudo APC alheri ne, kuma in ya shigo ba shi kadai ne dan PDP da ya dawo APC ba, akwai ire-irensu da dama da suka dawo kuma abin ya zama alheri. Mu dai fatarmu a samu kyakkyawan shugabanci a Jihar Kebbi da kasa baki daya, ba irin wannan bakin mulki da talauci da rashin adalci da kunci da zalunci da sata da ake yi a Jihar Kebbi da kasa baki daya ba.
Aminiya: Kana ganin APC za ta yi tasiri a kananan hukumomin Jihar Kebbi?
Sani Dodo: Duk kananan hukumomin Kebbi 21akwai shugabannin wannan jam’iyya ta APC, kuma talakawa da masu kishin kasa sun shiga wannan jam’iyya kamar yadda ake shiga kasuwa domin kashi 95 a cikin 100 na ’yan Najeriya ba sa tare da PDP. Misali jihohin Kano da Sakkwato suna daga cikin jihohin da suka samu ci gaba da bunkasar tattalin arzikin kasa sakamakon iya gudanar da shugabanci na Gwamna Kwankwaso da Wamakko.  Amma in ka shigo Jihar Kebbi yadda ka san an yi yaki an watse ba ka ganin kowa sai mabarata maza da mata suna bin gefen titi. Duk da kason da Jihar Kebbi ke samu daga Asusun Tarayya amma ruwan famfo ya gagari talaka, ma’aikata suna cikin kuncin rashin ba su hakkokinsu, duk wanda ka gani sai ka ga kamar ya kamu da cutar Ebola. Al’umma na fuskantar mawuyacin hali saboda gwamnati ta kasa kyautata rayuwar talaka. Gwamnatin dakingari ta kamu da cutar Ebola saboda babu abin da ke motsawa a fadin jihar. Da yawa ’yan kasuwa sun samu karayar tattalin arziki saboda babu ciniki, ma’aikata kowa gani sai ka ga kamar zai daga hannu sama ya yi ihu. An kashe kananan hukumomi duk karamar hukumar da ka je ranar aiki sai ka ga bai fi mutum biyar su ma masinjoji da leburori kadai suke zuwa aiki, idan ka ga sakatariya ta cika to za a yi albashi ne. Rabon da ma’aikatan kananan hukumomi su je wurin semina a Jihar Kebbi tun lokacin Gwamna Adamu Aliero.
Yanzu baya ga albashi ba a ba su ko sisin kwabo a kullum shugabannin kananan hukumomi baya suke yi kamar wadanda EFCC ke nema domin babu komai a asusun ajiyarsu. PDP ta kawo bakin talauci da yunwa a Jihar Kebbi da Najeriya, yau ba wanda ya isa ya bar kofar gidansa a bude, kowa yana tafiya yana dar-dar ’yan fensho sun shiga halin lahaula wala kuwwata, karin albashi ya gagara ga ma’aikata.
Aminiya: Amma tana giggina makarantu da asibitoci da filin jirgi da hanyoyi ba ka gamsu da ayyukan da ta yi a cikin shekara bakwai ba?
Sani Dodo: To wadannan ayyuka da ka lissafa yadda kasan daurin zaren ’yan bori ne, bari mu fara da gina makarantu kamar yadda ka ce an yi, maimakon makarantun da muke da su a inganta su da kayan aiki da kwararrun malamai a gyara dakunan kwanan dalibai a kara giggina dakunan karatu. Amma ba a yi haka ba sai kawai aka ci gaba da giggina sababbin makarantu kuma har zuwa yanzu ba a bude ko guda ba iyaka kadangaru da macizai da beraye ke karatu a ciki. Idan ka duba ta fannin kiwon lafiya, yanzu haka Asibitin Sa Yahaya da ke cikin Birnin Kebbi kwararren likita daya ne kawai, sauran likitoci duk sun gudu saboda ba a biyansu hakkokinsu, duk asibitocin Jihar Kebbi ba likitoci, ba magani ba tsabta, idan ma ba ka yi hankali ba maimakon ka samu laifiya sai ciwo ya karu saboda rashin tsabta.
Aminiya: To me za ka ce game da filin jirgi da dakingari ya gina?
Sani Dodo: Wannan filin jirgin ba dakingari ya gina shi ba, Gwamna Adamu Aliero ne ya gina shi, dakingari kwaskwarima ya yi masa kan kudin da ya wuce na wasu jihohi da aka gina musu sababbi, domin kwaskwarimar ta share wajen Naira biliyan 17.  Jama’ar Jihar Kebbi ba filin jirgi ne damuwarsu ba, wadannan biliyoyin Naira da aka kashe ko in ce aka yi kashe-mu-raba da kamfanoni aka bude aka samu raguwar talauci da muke fama da shi a jihar da ya fi, yanzu Jihar Kebbi ba ta da ko kamfanin yin kofin roba.
Aminiya: Mene ne hasahenka kan zaben 2015?
Sani Dodo: Talakawan Jihar Kebbi ko ba a fada musu ba, sun san mai fisshe su, lokacin da aka kawo APC Jihar Kebbi yawan jama’ar da suka yi tururuwa domin yin rijista da ita na da ban mamaki. Kuma da hukumar zabe ta raba katin zabe na dindindin, idan ka ga dimbin jama’a da suka fito sai abin ya ba ka mamaki. Wannan na daya daga cikin yunkurin kawo canji a zabe mai zuwa domin jama’a sun gaji da mulkin PDP. Janar Muhammadu Buhari ya taba cewa jiki magayi kowa ya ga sakamakon muguwar gwamnati a Jihar Kebbi da Najeriya, saboda kashi 95 cikin 100 na magidanta a jihar ba sa cin abinci sau uku a rana. Kwamishina a Jihar Kebbi yana ganin darajar Naira dubu biyu, duk mai hankali ya san APC ce za ta ceto ’ya Najeriya daga halin da suke fuskanta na matsalolin rayuwa. Kowa ya ga sakamakon karbar omo da Naira 200 da turmin zane a lokacin zabe.