Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ba wa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ke jihar wa’adain kwana 30 zai kwace kadarorinsu saboda kin biyan haraji.
A ranar Laraba ce Gwamnatin Jihar Borno ta sanar cewa za ta fara kwace kadarorin wasu hukumomi bakwai na Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a jihar, saboda rashin biyan haraji.
- Gwamnatin Kwara ta gargadi makarantu kan hana sanya Hijabi
- Tallafin mai: Dole ’yan Najeriya su yi murna —Kungiyar Kwadago
“Sanarwar da aka ba su za ta halasta wa hukumar amfani da karfinta wajen kwace kadarorin hukumomin da abin ya shafa,” inji shi.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya bakwai da gwamnatin Bornon za ta kwace wa kadarori su ne: Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Shirin Samar da Abinci na Duniya (WFP), da kuma Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR).
Mohammed Alkali ya bayyana cewa, “Ya kamata a fahimci cewa hukumomin nan an tsame su daga biyan haraji daga kudaden aikinssu.