✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Borno za ta fara gine-gine a tsohon sansanin Boko Haram

A shekarar 2014, garin Gudumbali ya fuskanci harin farko na Boko Haram.

Gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar da shirinta na sake dawo da zamantakewa a garin Gudumbali, tsohon sansanin mayakan Boko Haram wanda kwanan nan sojojin Najeriya suka kwato.

Kwamishinan Ma’aikatar Gyara Muhalli na Jihar (MRRR), Injiniya Mustapha Gubio, ne ya bayyana hakan ne bayan wata ziyara da ya kai garin Gudumbali, Hedikwatar Karamar Hukumar Guzamala ta Jihar Borno.

A yayin kaddamar da kwamitin sake gina matsugunan jama’a a watan da ya gabata, Gwamna Babagana Zulum ne ya bukaci sojoji da su kwato garin Gudumbali domin a samu damar sake ginawa da kuma gyara matsugunan jama’a.

A shekarar 2014, garin Gudumbali ya fuskanci harin farko na Boko Haram, inda aka tilasta wa mazauna garin tserewa zuwa Monguno da Maiduguri.

A shekarar 2018 aka sake tsugunar da jama’ar garin Gudumbali, amma bayan wata uku ‘yan Boko Haram suka sake korarsu.

Injiniya Gubio, ya ci gaba da cewa a yanzu da aka kwato garin abin da kwamitin zai fara yi shi ne samar da rundunar soji a Gudumbali ta yadda za a samu nasarar sake yin gine-gine da tsugunar da jama’a cikin kankanin lokaci.