✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Borno ta fara shirin daukar sabbin malaman makaranta 3,000

Gwamnatin Borno za ta dauki ma'aikatan ne domin ci gaba da inganta fannin ilimin jihar.

Gwamnatin Jihar Borno, ta bude shafin intanet da za a yi amfani da shi don neman gurbin aiki a sabbin malaman makaranta 3,000 da za ta dauka.

Sanarwar da ta fito ta hannun Mukaddashin Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi ta jihar, Ali Musa, ta bukaci masu sha’awar aikin kuma suka cancanta, da su je su shigar da bayanansu ta wannan adireshin na intanet: moeapplication.bornostate.gov.ng

Daga cikin sharuddan cancantar neman aikin kamar yadda sanarwar ta nuna, ban da wadanda suka haura shekara 50 da haihuwa.

Sanarwar ta ce za a rufe shafin neman aikin ne ya zuwa 31 ga Disamba, 2022.

Gwamnatin Borno, karkashin Gwamna Babagana Zulum, ta dauki matakin daukar sabbin malaman ne domin inganta fannin ilimin jihar.

(NAN)