Shugaban Kwamitin Mafi Ƙarancin Albashi na Jihar Borno, Dokta Babagana Mallambe, ya sanar da cewa ma’aikatan gwamnatin jihar sun fara karɓar sabon albashin Naira 70,000.
Gwamnatin ta ƙara albashin be don ƙarfafa gwiwar ma’aikata da kuma inganta rayuwarsu ta fuskar tattalin arziƙi.
- Ku daina tsine wa shugabanni, ku bar su da Allah — Sarkin Musulmi
- Ba za a dawo da tallafin man fetur ba — Minista
A wani taron manema labarai da ya gudanar a Maiduguri a ranar Litinin, Dokta Mallambe, wanda shi ne Kwamishinan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare, ya tabbatar da fara biyan sabon albashin.
“Ina farin cikin sanar da ku cewa an samu nasarar aiwatar da mafi ƙarancin albashin Naira 70,000 ga ma’aikatan gwamnati a Jihar Borno.
“Wannan babban ci gaba ne kuma yana nuna jajircewar Gwamna Babagana Umara Zulum wajen tallafa wa ma’aikatan jihar,” in ji shi.
Dokta Mallambe, ya bayyana cewa ƙarin albashin zai inganta rayuwar ma’aikatan gwamnati da iyalansu, ya kuma ƙara musu ƙwarin gwiwa, kuma zai bunkasa tattalin arziƙin jihar.
Shugaban Ma’aikatan jihar, Barista Fannami, ya ƙara da cewa kwamitin ya bi dokokin mafi ƙarancin albashi da kuma daidaita biyan albashin daidai da yanayin tattalin arziƙin jihar.
Ya buƙaci ma’aikatan gwamnati su ƙara himma a aikinsu, su gode wa gwamnan jihar bisa goyon bayansa na ƙara albashin.
Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago na jihar, Kwamared Inuwa, ya jinjina wa gwamnatin jihar kan aiwatar da sabon albashin.
Amma ya roƙi gwamnatin da ta faɗaɗa ƙarin zuwa ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar 27 domin inganta rayuwarsu.