✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Bauchi ta sayi fom din JAMB na Naira miliyan 29

Gwamnatin Jihar Bauchi ta sayi fom na jarrabawar shiga jami’o’i da manyan kwalejoji (UTME) na kimanin Naira miliyan 29 domin raba wa daliban da suka…

Gwamnatin Jihar Bauchi ta sayi fom na jarrabawar shiga jami’o’i da manyan kwalejoji (UTME) na kimanin Naira miliyan 29 domin raba wa daliban da suka kammala makarantun sakandare a jihar.

Da yake jawabi a yayin rarraba fom-fom din ga dalibai 5000, Kwamishinan Ilimi a jihar, Farfesa Haruna Abdullahi Danwaka ya bayyana cewa an samar da fom-fom din ne ga daliban jihar da suka yi kokari sosai a jarrabawar da aka gudanar masu ta gwaji.

Ya bayyana cewa daliban da suka samu yabo (kiredit) guda biyar da suka hada da darussan Inglishi da Lissafi ne aka zabo daga makarantun sakandare daban-daban da ke fadin jihar, domin raba masu fom din.

Ya kara da cewa wannan ne karo na farko da gwamnati ta samar da wannan garabasa ga daliban jihar.

A jawabin Shugaban Kwamitin Rarraba fom din, Alhaji Nuruddeen Abdullahi, ya yaba wa Gwamna Mohammed Abubakar da ya kirkiro wannan tsari, wanda hakan zai taimaka wa dalibai su samu guraben karo ilimi cikin sauki a manyan makarantu.

Alhaji Abdullahi, wanda shi ne Darakta mai kula da harkokin jarrabawa na Ma’aikatar Ilimi ta jihar ya yi kira ga daliban da suka ci wannan gajiya da iyayensu su yi amfani da wannan dama yadda ta dace.