✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Bauchi ta nada sabon Sarkin Jama’are

Alhaji Nuhu Ahmad Wabi ya maye gurbin mahaifinsa da ya rasu a farkon watan Fabrairu.

Gwamnatin Jihar Bauchi ta nada Alhaji Nuhu Ahmed Wabi a matsayin sabon Sarkin Jama’are.

Sabon sarkin ya maye gurbin mahaifinsa, Alhaji Ahmad Mohammed Wabi, wanda ya rasu a farkon watan Fabrairu.

Sanarwa nadin sabon sarkin na dauke ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Ibrahim Alkassim Mohammed, ya fitar a ranar Litinin.

Alhaji Nuhu Ahmad Wabi ya kasance sarki na 10 da ya dare bisa karagar mulkin Masarautar Jama’are.

Kafin nadin nasa a matsayin sabon sarkin, shi ke rike da sarautar Yariman Jama’are.

Tuni al’ummar Jama’are suka shiga shewa da murna, bayan fitar sanarwar nadin sabon sarkin.