Gwamnatin jihar Bauchi ta warware rawanin masu sarautun gargajiya guda shida bisa samunsu da laifin saɓa wa dokokin aiki.
Hukumar kula da ma’aikatan ƙanann hukumomi ce ta sallame su bayan samunsa da ‘tsoma kai cikin harkokin siyasa’ da kuma wasu laifuffukan na dabam.
Sarakin da aka sauke sun haɗa da Alhaji Aminu Muhammad Malami, Hakimin Udubo, Alhaji Bashir Kabir Umar, Hakimin Azare, Umar Omar, Dagacin Gadiya, da Umar Bani Dagacin Tamasawa duk a Masarautar Katagum.
Gwamnan Bauchi ya jagoranci Sallar rokon ruwa
Majalisar Dokokin Bauchi za ta fara amfani da Hausa a yayin zamanta
Daga Masarautar Bauchi kuma akwai Bello Sulaiman, Dagacin Beni da Alhaji Yusuf Aliyu Badara, Dagacin Badara.
Muƙaddashin babban sakataren hukumar, Nasiru Ibrahim ne ya sanar da sauke masu sarautun gargajiyar.
Sanarwar ta umarci waɗanda aka sauke su miƙa takardun ajiye mulki ga sakatarorinsu kuma ta buƙaci masarautun da abin ya shafa su naɗa waɗanda za su kula da yankunansu kafin hukumar ta naɗa sababbi.