Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta bankado ma’aikatan bogi har guda 2,116 dfa ke karbar albashi a jihar.
A jawabinsa ga taron kiwon lafiya na farko da Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta shirya, Gwamnan Bala Mohammed ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci dage da kokarinta na bankado ma’aikatan bogi domin ceto sauran ma’aikatun a jihar daga shiga wani hali.
- Arewa ake neman karyawa da zanga-zangar #EndSARS —Sheikh Jingir
- #EndSARS: ‘Yan daba sun balle gidan yari, fursunoni dama sun tsere
- Ni matar manya ce ba ta yara ba —Rashida Maisa’a
“A ci gaba da kokarin da muke yi na karkade ma’aikatan bogi daga ciki tsarin biyan albashi a jihar nan, mun sake samun nasarar bankado wasu ma’aikatan bogi har 2,116.
“Daga cikinsu har da liktoci guda 100 da suke aiki a kananan asibitoci sai kuma ragowar ma’aikatan lafiya da ke aiki da kungiyoyi masu zaman kansu daban-daban, amma kuma suke ci gaba da karbar albashin jihar nan duk da cewa sun daina aiki”.
“Saboda haka ne gwamnatin jihar Bauchi ta shirya domin yin ayyuka daban-daban domin kawo gyara a harkar lafiya tare da rage mutuwar kananan yara”, cewar gwamnan.
A yayin da yake gabatar da nasa jawabin, Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire, ya bayyana cewa taron na da matukar muhimmanci kuma ya zo a daidai lokacin da ya dace.
Ministan ya sake jinjina wa gwamnatin jihar bisa yadda ta ba wa harkar kiwon lafiya muhimmanci.