Gwamnatin Amurka ta bukaci jami’an diflomasiyarta da ke aiki a Abuja, babban birnin Najeriya da su fice daga garin domin kaucewa hare haren ta’addancin da tace akwai yiwuwar aukuwarsu.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta gabatar da wannan sanarwa wadda ta bukaci ficewar jami’an diflomasiyyar da ayyukansu ba su zama wajibi ba da su fice tare da iyalansu saboda karfin barazanar da suka ce birnin na fuskanta.
- INEC ta ayyana ranar zabukan jihohin Bayelsa da Imo da Kogi
- Matasan da suka karkatar da kayan N25m sun shiga hannu
Ita dai wannan sanarwar ba ta bayyana shirin kwashe jami’an diflomasiyar ba, amma ta yi gargadi ga Amurkawa akan kaucewa tafiye tafiyen da basu zama wajibi ba zuwa Najeriyar kanta.
Amurkar ta fidda wannan sanarwar ce saboda damuwar da take da ita akan aikata laifuffuka da kuma rashin kwanciyar hankali.
Wannan gargadin na zuwa ne kwana biyu bayan wadda ta gabatar a karshen mako wanda yake cewa akwai yiwuwar kai harin ta’addanci a birnin Abuja.
Tuni dai wasu kasashen Yammacin Duniya irinsu Birtaniya da Canada da kuma Australiya suka gabatar da irin wannan gargadi.
Gwamnatin Amurkan ba ta yi cikkaken bayani akan irin barazanar birnin na Abuja da ke dauke da mutane sama da miliyan 6 ke fuskanta ba.
Sai dai masana harkar tsaro na danganta wannan gargadi da karuwar hare haren ’yan ta’adda a Najeriya musamman ganin yadda suka fasa gidan yarin Kuje suka kuma fitar da wasu abokan aikinsu a watannin da suka gabata.
Sai dai Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta bukaci jama’ar kasar da su kwantar da hankalinsu, inda tace tana aiki tare da wasu hukumomin tsaro domin kare lafiyar jama’ar birnin da kuma kasa baki daya.