Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Sakkwato, Alhaji Ibrahim Adare ya ba da tabbacin in dokar da ke gaban Majalisar Dokokin Jihar ta samu amincewa, gwamnatin jihar za ta yanka wa hakimai albashi.
Kwamishinan ya bayyana haka ne a wajen sauraren ra’ayoyin jama’a kan kudurin dokar a zauren Majalisar Dokokin Jihar da aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata.
- ’Yan bindiga sun sace ’yan jarida da iyalansu a Kaduna
- ‘Yan Arewa za su samu albarka a Kasuwar Ogere — Sarkin Ogere
Ya ce, “Idan muka dubi kudirin dokar da aka gabatar a yau, za mu fahimci lamarin a tarihi, sarakuna da hakimai ana yin maganarsu lokaci-lokaci.
“Ko a lokacin mulkin mallaka ana neman Gwamna don ya bayar da amincewarsa wajen nada su.
“Haka lamarin yake har lokacin mulkin soja, a lokacin mulkin Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa yana Gwamna aka daga darajar Masarautar Sarkin Musulmi.
“A lokacin Sanata Aliyu Magatakarda aka canja tsarin aka bai wa Majalisar Sarkin Musulmi damar nada kananan hakimai.
“Haka lamarin ya zo har lokacin Sanata Aminu Waziri Tambuwal.
“A yau a wannan gwamnati ta Ahmad Aliyu aka fahimci akwai kurakurai nan da can, aka ga ya dace a yi wa dokar gyaran fuska domin a daga darajar sarakanunan a addinance da al’adance da kuma ta fuskar tattalin arzikinsu.
“Haka kuma, in hakimai Gwamna ne ya nada su, dole ne ya yanka masu albashi, domin dan abin da ake ba su ba ya biyan bukatunsu.
“Haka ma a gefen martabarsu, idan Gwamna ne yake nada su, za ka ga ke nan sun samu kusanci da Gwamna da gwamnati, ita gwamnati za ta zama kusa da su.,” in ji shi.
A bangaren, Kwamishinan Shari’a na Jihar Sakkwato, Muhammad Nasiru Binji ya ce, Sarkin Musulmi ba ya da hurumin da zai nada hakimai da uwayen kasa, ba tare da tuntubar Gwamna ba.
Ya ce, “Sashe na 76(2) na dokar kananan hukumomi da sarakuna ta bai wa Sarkin Musulmi karfin ikon ya nada uwayen kasa da hakimai a jihar bisa ga amincewar Gwamna mai ci ne.”
Da yake bayanin kan lamarin, Alhaji Shehu Kakale Shuni, Shugaban Kungiyar Sakkwatawa Mu-Koma-Tushe, ya ce, “Ba mu goyi bayan duk wani abu da zai kawo tarnaki ko rashin walwala ga Masarautar Mai alfarma Sarkin Musulmi ba.
“A takaice dai wannan kudirin doka ba mu goyon baya, in har wani abu za a yi, sai dai a kara wa wannan majalisa karfi, ba wai a rage ba.
“Mai girma Sanata Wamakko shi ya yi wannan gyara kamar yadda magabata suka fada.
“Muna kira ga majalisa a yi amfani da idon basira a kara wa Majalisar Mai alfarma Sarkin Musulmi karfi ba ragewa ba.”
Shi ma Shehu Garba Takatuku ya ce, wannan sauraron jin ra’ayin jama’a “An yi mana zalunci, abin da doka ta tanada a kira mutane a saurari ra’ayinsu, amma an kira mun zo ba a saurare mu ba.”
Ya kalubalanci maganar Kwamishinan Shari’a, inda ya ce bai fahimci yadda kundin tsarin doka yake magana ba.
“A madadin kungiyarmu ta Muhajiruna da Lansaru ta dangin Mujaddadi Shehu Dan Fodiyo za mu dauki mataki, ba mu yarda da wannan dokar ba, za mu tafi kotu,” in ji shi.
“Bai kamata gwamnonin Arewa su rika cin zarafin sarakunanmu ba, bayan sun mayar da hankali ga harkar tsaro da tattalin arzikinmu, amma sun koma duba wani abu daban na karbe aikin wasu.
“Sarakuna ne ake jin maganarsu, ake girmamawa, masarautar Sarkin Musulmi cibiya ce ta addinin da al’adarmu, duk wanda ya ce ba zai yi da masarauta ba, ba za mu yarda ba.”
Kwamared Kasim Na -Kura, Shugaban Kungiyar Matasan Arewa ya ce, “Ba mu yarda dokar da ake son a rage wa Sarkin Musulmi karfin iko ba.
“Muna so kada majalisa ta amince da haka domin rage wa majalisar daraja da kima ne a idon jama’a.”