✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnati za ta rage kashi 30 na cunkuso a gidajen gyaran hali

Rage cunkoso a gidajen gyaran hali 253 da mu ke da su a fadin kasar nan ya zama dole.

Gwamnatin Tarayya na shirin sakin akalla kashi 30 na adadin fursunonin da ke tsare a gidajen gyaran hali a fadin kasar.

Ministan Kula da Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da haka a hirar da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a Abuja.

Ministan ya ce yawan wadanda ake tsare da su a gidan gyaran hali ya kai 75,635, kashi 70 daga cikinsu ana yi musu shari’a ne, a bisa kananan laifuka da kuma karya dokokin jihohi.

A kan haka ne ya ce Ma’aikatarsa ke shirin tattaunawa da gwamnonin jihohi domin ganin yadda za a yi a sako mutanen da ake tsare da su, musamman wadanda ke jira a yanke musu hukunci domin a rage cunkoso.

“Rage cunkoso a gidajen gyaran hali 253 da mu ke da su a fadin kasar nan ya zama dole, saboda wasu da yawa bai kamata a tsare su [tsawon lokaci] ba.

“Idan ka kama barawo da laifin ‘yar karamar sata, amma ka tsare shi tsawon shekara 3 ka na yi masa shari’ar da hukuncin daurinsa bai wuce wata 6 ba, babu fa’ida,” a cewar Aregbesola.

Kazalika, ya ce ya rubuta wa Kungiyar Gwamnoni kan bukatar ta halarci taronsu, inda za a tattauna kan kan wannan matsalar da kuma yadda za a shawo kanta.

Ministan ya kuma da cewa, dole ne duk masu ruwa da tsaki a kasar nan su zo a zauna a gyara tsarin hukunta masu laifi, idan ba haka ba, ba za a rabu da matsalar cunkoso a gidajen gyaran hali na kasar nan ba.

%d bloggers like this: