Gwamnatin Tarayya ta fitar da Naira biliyan 75 don bai wa matasa bashin dogaro da kai.
Ministan Matasa da Wasannin, Sunday Dare ya bayyana haka a jawabin da ya yi wa ‘yan jarida a fadar shugaban kasa, ranar Laraba.
Dare ya ce, an kirkiri Bankin Matasa da zai taimaka wajen wayar da matasan Najeriya miliyan 68 masu shekara 18 zuwa 35 a kan harkar kasuwanci.
Ya kuma shawarci matasan da suke da tunanin wani kasuwanci da su tuntubi kananan bankuna da ke bayar da bashi guda 125 a fadin kasar nan don karbar jari ga wadanda suka cancanta.
Dare ya bayar da tabbacin cewa za a yi adalci ga matasan wajen gudanar da shirin da za a aiwatar ta fasahar intanet.
Ya ce kowa zai iya samu ba tare da bangarancin addini ko kabilanci ba.