Gwamnatin Tarayya za ta gina wa daliban Jami’ar Bayero da ke Kano gadar sama da za su rika tsallakawa zuwa cikin jami’ar don saukaka musu.
Za a yi wannan yunkuri ne don rage yawan samun hatsari yayin tsallaka titi da daliban jami’ar ke yi lokaci bayan lokaci.
- Yadda mafarauci ya kashe makiyayi a Ogun, ya birne shi a daji
- Natasha Hadiza Akpoti: Jagorar gwagwarmaya da kasuwanci
Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ne, ya bayyana hakan lokacin da ya ke bude aikin wani titi mai nisan kilomita daya da rabi da Gwamnatin Tarayya ta samar a cikin jami’ar.
Ministan, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatar ayyuka na kasa reshen Jihar Kano, Injiniya Yahaya Baba Ali, ya ce yanzu haka gwamnati ta fara samar da manyan hanyoyin zirga-zirgar ababen hawa masu inganci a manyan makarantun kasar nan, domin kara inganta harkokin koyarwa da kuma kiyaye rayukan dalibai.
Tun farko jami’ar Bayero ce ta kai kokenta ga gwamnatin kan barazanar da dalibai ke fuskanta yayin tsallaka titi, wanda hakan ya sa ta bukaci samar da gadar da za ta saukaka wa daliban.
Da ya ke nasa jawabin, Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya yabawa gwamnatin bisa yadda ta karbi koken da suka kai mata musamman na lalacewar wasu daga cikin hanyoyin jami’ar, wanda kuma ta fara sabunta su tare da samar da wasu sabbi.
Kazalika, Abbas ya ce a yanzu haka Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da samar da hanyoyin sufuri a jami’ar.