✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnati za ta fara daure Iyayen mabarata a Edo

Ilimin firamare hakkin kowanne yaro ne a Edo.

Gwamnatin Jihar Edo ta bayyana shirinta na soma daure iyayen kananan yara mabarata da ke gararamba da yawon barace-barace a fadin jihar.

Gwamnan jihar Godwin Obaseki ne ya bayyana hakan yayin da yake karbar bakin da suka kai masa ziyara fadarsa ranar Litinin.

Ya yi barazanar tsare duk iyayen da suka ki sanya ‘ya’yansu a makaranta suka kuma dora su kan mummunar dabi’ar yin bara a tituna.

“Gwamnatina ta yi imanin ilimin firamare hakkin kowanne yaro ne a Edo, sannan ga filayen noma amma babu masu yi” in ji shi.

Ya ce gwamnatinsa za ta fatattaki masu bara kwata-kwata a jihar nan da wasu kwanaki.

Don haka ya ce duk wanda gwamnatin ta kama yana bara a titi za ta maida shi gona yayi noma.

Dangane da batun karancin malaman makaranta a jihar ya ce gwamnatinsa ta debi karin ma’aikata 3,062 a kauyuka domin inganta ilimin.