Gwamnatin Jihar Edo ta bayyana shirinta na soma daure iyayen kananan yara mabarata da ke gararamba da yawon barace-barace a fadin jihar.
Gwamnan jihar Godwin Obaseki ne ya bayyana hakan yayin da yake karbar bakin da suka kai masa ziyara fadarsa ranar Litinin.
- Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 4 a Benuwe
- Kungiyar dalibai ta yi barazanar kawo cikas a zabukan APC da PDP
Ya yi barazanar tsare duk iyayen da suka ki sanya ‘ya’yansu a makaranta suka kuma dora su kan mummunar dabi’ar yin bara a tituna.
“Gwamnatina ta yi imanin ilimin firamare hakkin kowanne yaro ne a Edo, sannan ga filayen noma amma babu masu yi” in ji shi.
Ya ce gwamnatinsa za ta fatattaki masu bara kwata-kwata a jihar nan da wasu kwanaki.
Don haka ya ce duk wanda gwamnatin ta kama yana bara a titi za ta maida shi gona yayi noma.
Dangane da batun karancin malaman makaranta a jihar ya ce gwamnatinsa ta debi karin ma’aikata 3,062 a kauyuka domin inganta ilimin.