Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta binne wasu gawarwaki 49 a rami daya idan ’yan uwan masu su ba su zo sun tafi da su ba.
Gwamnatin ta ce za ta yi hakan ne bayan wa’adin kwana biyar da ta ba wa dangin mamatan su dauke su daga mutuwarin Babban Asibitin Sabon Tasha da ke Karamar Hukumar Chikun ta jihar.
- An ceto leburori 25 da bene mai hawa 7 ya rushe a kansu a Legas
- Shekara 9 da sace Daliban Chibok, har yanzu 98 na hannun Boko Haram
Shugaban Karamar Hukumar Chikun, Salasi Nuhu Musa, ya ce an kai gawarwakin asibitin ne a lokuta daban-daban daga ofishin ’yan sanda na Kasuwar Magani da kuma na Toll Gate.
A cewarsa, “An iya gane 25 daga cikin gawarwakin 49, ragowar 24 kuma ba a gane su ba saboda ba sa dauke da wata alamar shaida a lokacin da aka kawo su mutuwarin.
Ya kara da cewa tuni karamar hukumar ta samu amincewar gwamnatin jihar domin binne gawarwakin, wanda zai gudana a mako mai zuwa.