✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati za ta ba Pillars garabasar Naira miliyan daya idan…

An shawarci Hukumar Gudanar da Gasar Premier ta kasa da ta dauki kwakkwaran mataki domin kaucewa faruwar wasu daga cikin irin matsalolin da suka faru…

An shawarci Hukumar Gudanar da Gasar Premier ta kasa da ta dauki kwakkwaran mataki domin kaucewa faruwar wasu daga cikin irin matsalolin da suka faru a gasar bara. Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima ne ya yi wannan kiran yayin da Shugaban Yan wasa na kungiyar Wasan kwallon kafa ta Kano Pillars da Masu koyar da ’yan wasan suka ziyarce shi a ofishinsa.

Alhaji Galadima ya bayyana cewa Gwanmatin Jihar Kano ta yi alkawarin bai wa ‘yan wasan Kano Pillars da masu horar da su garabasar Naira miliyan daya a duk lokacin da suka yi nasara a wasannin firimiyar da za a fara a jibi Lahadi.

Shugaban Hukumar Wasanannin ya kara da cewa gwamnatin ta yi haka ne don kara bunkasa kwazon ’yan wasan wajen ganin ta ci gaba da kare kanbunta na samun nasara a wasannin.

Alhaji Galadima ya jaddada cewa Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje a shirye yake ya yi duk mai yiyuwa wajen ganin kungiyar “Sai masu gida” ta koma kan gwadaben da aka san ta na samun nasara a duk wasanmnin da za ta fafata a bana. 

Alhaji Ibrahim Galadima ya yaba wa kungiyar Kano Pillars inda ya bukaci su ci gaba da nuna kwazo don samun nasara a kakar wasa ta bana.

A nasa jawabin tun da farko Shugaabn kungiyar Kano Pillars Alhaji Tuklur Babangida ya bayyana cewa sun je wurin shuagabn ne don su nuna masa kofunan da kungiyar Pillars ta samu nasarar lashewa a gasanni uku da suka fafata da suka hada da kofin da suka lashe a Jihar Kwara da wanda suka samu a Jihar Kano sai kuma gasar kofin Ahlan da suka samu nasara a kwanan nan.

Alhaji Tukur Babangida ya bayyana cewa yanzu sun yi wa ‘yan wasa 34 rajista don tunkarar gasar ta bana, sannan ya sha alwashin kungiyar ba za ta ba gwamanti da al’ummar Jihar Kano kunya ba.