Gwamnatin Tarayya ta amince da yi wa ’yan sanda karin albashi da kaso 20 cikin 100.
Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dingyadi, ne ya bayyana hakan ranar Laraba, bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta kasa na wannan makon.
- Fadan cikin gida ya fara kamari a tsakanin ’yan bindiga a Katsina
- Majalisa ta amince wa Buhari ya ciyo sabon bashin $5.8bn
Ya ce karin zai fara aiki ne daga watan Janairun 2022.
A cewar Ministan, karin na cikin abubuwan da masu zanga-zangar #EndSARS suka bukata, wanda ke da alaka da walwalar ’yan sanda.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne ya jagoranci taron, ya ce za a kara albashin ne don ya dace da ayyukan da suke yi da kuma karfafa yunkurin samar da zaman lafiya a kasa.
Ministan na ’Yan Sanda ya ce za a yi karin ne ta hanyar dada musu kudaden alawus-alawus dinsu da kaso shida cikin 100, da kuma karin Naira biliyan 1.1 don biyan basussukan da suke bi na tsakanin shekarar 2013 zuwa 2020.
Kazalika, Majalisar Zartarwar ta kuma amince da fitar da Naira biliyan 13.1 don biyan kudaden sallamar ’yan sanda 5,472 da suka mutu daga tsakanin shekarar 2013 da watan Agustan bana.