✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnati ta yi gwanjon rigar nonon Diezani a kan $12.3m

Tuni dai aka dauko dillalai 613 da za su yi aiki cefanar da kayan.

Daga cikin irin kadarorin da Gwamnatin Tarayya ta ke gwanjonsu mallakin tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Alison-Madueke, an bayyan cewa har da wasu rigunan nonon da darajarsu ta kai kusan Dalar Amurka miliyan 12.3.

Tsohuwar Minsitar dai wacce ta rike mukamin zamanin tshohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ta cika wandonta da iska ta bar Najeriya jim kadan da barinsu mulki a 2015.

Ana zarginta dai da karkatar da kudaden da yawansu ya kai kimanin Dala biliyan 2.5 a lokacin da take Minista, ko da yake ta sha musanta hakan.

Tuni dai Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta fara yunkurin dawo da ita Najeriya don ta fuskanci shari’a.

Kazalika, Gwamnatin Tarayya ta sami amincewar kotu wajen kwace kadarorin Diezanin da suke unguwannin Banana Island da rukunin gidajen Foreshore da Ikoyi, duk a Jihar Legas, ciki har da wasu manyan gidaje guda 18.

Sauran kayayyakin da aka yi gwanjon nasu sun hada da manya da kananan rigunan biki na alfarma guda 138, gajerun wandunan motsa jiki guda 41, wasu kayan sawa guda 73 da sut-sut guda 11 da kuma rigunan nono na alfarma guda 11.

Sauran sun hada da mayafai guda 73, kananan rigunan nono guda 30, sikel 17, mayafai bakwai da kuma takalma 64.

Tuni dai gwamnatin ta fara tantance wasu dillalai kimanin 613 da za su Kula da sayar da kayayyakin da aka kwace.