✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta tsaida ranar bude makarantu a jihar Neja

Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da cewa za ta bude makarantun firamare da na sakandire a ranar 4 ga watan Oktoban 2020 domin ci gaba…

Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da cewa za ta bude makarantun firamare da na sakandire a ranar 4 ga watan Oktoban 2020 domin ci gaba zangon karatu na uku na shekarar 2019/2020.

Kwamishinan Ilimi ta jihar, Hajiya Hannatu J. Salihu ce ta sanar da hakan a ranar Litinin tana mai kira ga makarantu sun tsunduma cikin shirin fara budewa tun daga gobe Talata, 29 ga watan Satumba.

Ta ce hukuncin hakan ya biyo bayan tattaunawar da ta yi da kwamitin da Gwamnatin Jihar ta kafa da ya kunshi dukkan masu ruwa da tsaki domin bijiro da ka’idodin bude makarantun cikin aminci.

Kwamishinan ta ce Gwamnatin Jihar ta dauki dukkanin matakan kariya gabanin bude makarantun bayan zaman tattaunawar Kwamishinonin Ilimi na Jihohi 19 da ke Arewacin Najeriya suka gudanar kan bude makarantun a garin Abuja.

Ta ce sabon zangon karatu na 2020/2021 zai fara ne daga ranar Lahadi, 3 ga watan Janairun 2021 yayin da ta ke kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da rataya a wuyansu.

A daya daga cikin matakan dakile yaduwar cutar Coronavirus, Gwamnatin Tarayya tun a watan Maris ta bada umarnin rufe kafatanin makarantu a duk fadin kasar.