✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta tara Naira biliyan 208 daga albashin ma’aikatan bogi

Gwamnatin Tarayya karkashin shirin shugaban kasa na bincikar tsarin biyan albashin ma’aikatan gwamnati ta tara Naira biliyan 208 daga albashin ma’aikatan bogi da ake biya.…

Gwamnatin Tarayya karkashin shirin shugaban kasa na bincikar tsarin biyan albashin ma’aikatan gwamnati ta tara Naira biliyan 208 daga albashin ma’aikatan bogi da ake biya.
 
An samu makuden kudin daga albashin ma’aikata na tsoffin jakadu da ragin kudin da ma’aikatu da hukumomin gwamnati suka rage da alawus-alawus na sojoji da sauran ma’ikatun da ke sanya kayan sarki da kuma ragin da aka samu na albashin ma’aikatan lafiya da makamantansu.
 
Da yake jawabi a karshen mako a wata bitar da aka gudanar a Abuja ga manema labarai da ke ruwaito labarun kudi wanda ma’aikatar kudi ta shirya, Sakataren kwamitin shugaban kasa na kididdige kudin gwamnati, Dokta Mohammed K. Dikwa ya ce a shekarar 2016 kwamitin ya tara jimillar Naira biliyan 97 da Naira biliyan 110 sakamakon namijin kokarin da suka yi.