Gwamnatin Tarayya ta shawarci ’yan Najeriya masu shirin zuwa Amurka da Ingila da sauran kasashen Turai da su yi hankali da barayin da za su iya yi musu sata a can.
Gwamnatin ta shawarci ’yan kasar tata da su yi takatsantsan da mutanen da za su iya sace musu fasfo da kudi da sauran muhimman abubuwansu a kasashen.
- Ban ga laifin masu barin Najeriya don neman ingantacciyar rayuwa ba – Kakakin Buhari
- Qatar 2022: Zafin cin kwallon Moroko ya haddasa tarzoma a Belgium
Minista Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayar da shawarar ranar Litinin, lokacin da yake jawabi kan nasarorin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a Abuja, karo na biyar.
A cewarsa, a dan tsakanin nan, ana samun karuwar rahotannin yawan sace wa ’yan Najeriya kayayyakinsu, ciki har da fasfo dinsu.
Lai Mohammed ya ce, “An jawo hankalin Gwamnatin Najeriya kan karuwar rahotannin sace wa ’yan kasarta kayayyaki a Amurka da wasu kasashen Turai, kayayyakin da suka hada da kudi da fasfo.
“A baya-bayan nan, wadanda lamarin ya fi shafa su ne wadanda suka tafi Ingila, inda akan sace musu kayayyaki musamman a manyan kantunan Oxford. Haka ce ta sa muka yanke shawarar gargadin ’yan Najeriya da ke kokarin zuwa wadannan kasashen don su yi takatsantsan.
“Ba mu cika bayar da irin wannan shawarar ba, saboda ba za ta yi wa ofisoshin jakadanci dadi ba da Ma’aikatar Harkokin Waje. Amma shawara ce ga ’yan Najeriya masu son tafiya wadaddan kasashen,” inji Lai Mohammed.
Shawarar na zuwa ne wata daya bayan kasashen Amurka da Birtaniya sun gargadi ’yan kasarsu cewa za a iya kai hari kan Abuja.
A lokacin dai Ministan ya yi watsi da gargadin, inda ya ce hatta Amurkan ba ta tsira daga kalubalen tsaro ba.