Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun 25 Talata da 26 Laraba ga watan Disamba a matsayin ranakun hutun bukukuwan Kirismeti.
Gwamnatin kuma ta bayyana ranar Talata 1 ga watan Janairu na shekarar 2019 a matsayin ranar hutun sabuwar shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Abdurrahman Bello Danbazau ne ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya.