Gwamnatin Tarayya ta sake shigar da karar jagoran masu fafutukar kasar Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu, kan wasu tuhume-tuhume guda bakwai da ta yi wa kwaswarima.
Wannan na zuwa kimanin wata daya bayan da Kotun Daukaka Kara ta wanke Kanu daga zarge-zargen da gwamnati ta yi masa a baya.
- Sojoji sun kashe gomman ’yan ta’adda a Zamfara
- Kalubale da Mata Masu Yoyon Fitsari ke Fuskanta A Cikin Al’umma
Binciken jaridar Vanguard ya gano cewa karar mai lamba: FHC/ABJ/CR/383/2015 da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, na kunshe da dukkan tuhume-tuhumen da aka yi wa Kanu a baya wanda kotu ta riga ta wanke shi a kansu.
Gwamnati ta yi zargin Kanu wanda a halin yanzu yake tsare a hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), a matsayinsa na mai jagorantar haramtacciyar kungiya, an ji yo muryarsa a wani shirin da aka yi da shi a rediyo ya yi barazanar zai gama da duk wanda ya ki bin umarninsa na hana kowa ya zauna a gida a yankin Kudu maso Gabas.
Gwamnati ta shaida wa kotun sakamakon barazanar da Kanu ya yi, hakan ya tilasta wa makarantu da kasuwanni da bankuna da gidajen mai da sauransu rufe harkokinsu a wasu jihohi da ke Kudancin Najeriya, tare da jefa jama’a cikin mawuyacin hali.
Haka nan, Gwamnati ta yi zargin wani lokaci tsakanin 2018 da 2021, an ji yo jagoran na IPOB cikin wani shirin rediyo yana ingiza al’umma a kan su yi farautar jami’an tsaron Najeriya da iyalansu su kashe.
Wannan laifin dai gwamnatin ta ce hukuncinsa na karkashin Sashe na 1 (2) (h) na Dokokin Hana Ta’addanci wanda aka yi wa gyara na 2013.
Kazalika, gwamnatin na zargin Kanu da bai wa mambobin IPOB umarnin su hada bama-bamai, da sauransu.
A baya, Kanu ya musanta tuhume-tuhumen da gwamnati ta yi masa.
Da ma dai Alkalin kotun, Mai Shari’a Binta Nyako, ta tsayar da ranar Litinin mai zuwa don lauyoyin bangarorin biyu su hadu su yi wa kotun bayanin yadda za a samu mafita kan batun.