✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnati ta rushe shagunanmu a ranar da ta ba mu wa’adi

Bayan awa shida da sanar da mu suka fara rushe shagunan da aka gina tun zamanin turawa

Wasu mahauta a dadaddiyar kasuwar nan mai dimbin tarihi ta Kurmi a Kano na zargin Karamar Hukumar Birni da Kewaye ta rushe musu shaguna a ranar da ta ba su wa’adin tashi.

Rahotanni sun nuna shagunan da yawansu ya kai 88 sun shafe sama da shekaru 120, kafin karamar hukumar ta rushe su a makon jiya a kokarinta na ‘sabuntawa da zamanantar da su’.

A zantawarsa da Aminiya, Mataimakin Shugaban Kungiyar Mahauta na kasuwar, Alhaji Nasidi Nafi’u Yahaya ya ce an yi rusau din ne ba tare da an ba su gargadin tashi ba.

“Da farko dai sun ce sun ba mu kwana uku mu tashi, amma bayan kamar sa’o’i shida na wannan ranar kawai sai suka dawo suka fara rushe-rushen ba tare da zuwa da ko da takarda guda daya dauke da umarnin yin hakan ba.

“Akwai shaguna 44 a bangarori biyun da aka rushe; shaguna 88 ke nan, kuma sun haura shekaru 120; Turawan mulkin mallaka ne suka gina su”, kamar yadda ya ce.

Alhaji Nasidi Nafi’u Yahaya

Ya yi zargin cewa: “Karamar Hukumar Birni da Kewaye karkashin jagorancin Alhaji Sabo Dantata ta hada baki da wasu baragurbin shugabanni na Kungiyar Mahautan Jihar Kano suka rushe wurin.

“A matsayina na mataimakin shugaban kungiyar nan na sama da shekara 28, ba mu da wata masaniya kan yinkurin ruguzau din.

— Sun yi watandar shagunan tun kafin a gina

“Sun je sun kawo ‘yan daba sama da 100 dauke da muggan makamai suka fid da mu ta karfin tsiya kafin su fara rushewar”, inji Alhaji Nasidi.

Mataimakin shugaban ya kuma yi zargin cewa tuni aka rabe shagunan tun ma kafin a fara gininsu ga wasu da ba ma a kasuwar suke ba.

Ya kuma ce tun bayan rusau din suke ta rabe-rabe a kofar shagunan makwabtansu, sakamakon tsugunar da su da rashin rumfunan ya yi.

Wani bangare na shagunan da aka rusa

Shi ma wani wanda lamarin ya shafa mai suna Alhaji Sharu Jibrin ya ce ya shafe sama da shekaru 65 a kasuwar.

— Zuciyata ta so ta buga; mun shiga garari

Ya ce da farko yaudar su aka yi da cewa su bayar da hotunansu da sunan za a gina musu wuraren wucin gadi; Kwatsam sai aka wayi gari wadanda ma suke cikin an rushe.

Ya ce, “Wata motar katafila ta zo nan cikin rakiyar ‘yan daba dauke da makamai a ranar da za a yi rusau din da kamar misalin karfe 10 na safe.

“Ko da suka shaida mana gwamnati ce ta turo su dole muka kauce mu ka bar wajen, ba yadda muka iya.

“Sai da suka yi fatali da kayayyakinmu kafin ma su fara rusau din.

“Saboda abin da su ka yi mana, sai da zuciyata ta so ta buga, sai jikokina ne suka kama ni suka kai ni gida, yanzu a takaice kusan ba mu da sana’a”, inji Alhaji Sharu.

Kazalika, wani wanda shi ma rusau din ya shafa mai suna Sunusi Musa ya ce ya shafe sama da shekaru 45 a kasuwar, kuma shi ma a wajen iyaye da kakanni ya gaji rumfarsa.

— Sun ce gwamna ne ya sa su

Ya kuma shaida wa Aminiya cewa masu aikin rusau din sun yi da’awar cewa Gwamna Ganduje da matarsa ne suke bukatar filin kuma suka sa a rushe shagunan.

“Muna kira ga Gwamna Ganduje, Khadimul Islam da ya shiga lamarin nan ya kawo mana dauki saboda mun shiga garari kuma mun rasa tudun dafawa,” inji Sunusi.

Daga karshe mahautan sun yi kira ga gwamantin jihar da ta kawo musu dauki, suna masu bayanin cewa akwai akalla mutane 500 da ke cin abinci a wurin wadanda matakin yanzu ya mayar da su abin tausayi.

A kan mataki na gaba da za su dauka kuwa, Sakataren kungiyar, Abba Abdullahi Sani Korau ya ce za su dauki matakin shari’a.

“A kan ka’ida mu ke zaune a wurin nan, ba mu taba karya wata dokar gwamnati ba kuma muna biyan haraji.

“Saboda haka mutukar ba a yi abin da ya dace ba za mu maka karamar hukumar a kotu”, inji shi.

‘Babu hannun gwamna a ciki’

To sai dai Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nesanta kansa da lamarin inda ya ce ba shi ma da masaniya a kai.

Mashawarcin Gwamnan Kan Harkokin Yada Labarai, Salihu Tanko Yakasai ya ce shagunan a karkashin hurumin Karamar Hukumar Birni da Kewaye suke.

Ya ce, “Da farko dai gwamna bai ma san da lamarin ba kuma ba ma ya karkashin huruminsa ya rusa kowane shago a kasuwar. Amma idan suna da korafi za su iya rubutowa su kawo mana mu duba”.

— Karamar Hukumar Birni ta yi gum

To sai dai duk kokarin Aminiya na jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar ta Birni da Kewaye, Alhaji Sabo Muhammad Dantata ya ci tura.

Shugaban bai daga kiraye-kirayen wayar da muka yi masa ba kuma bai amsa rubutattun sakonnin da muka tura masa ba.

Wakilinmu ya tafi takanas zuwa ofishinsa, inda ya tabbatar da cewa ya ga rubutaccen sakon da aka turo masa amma zai bayar da amsa daga baya.

Sai dai bai yi hakan ba har ya zuwa lokacin da muke kammala hada wannan rahoto.

Karamar hukumar dai ta yi suna wajen gine-gine da rushe-rushe a kasuwanni, inda a ‘yan shekarun baya aka ruwaito yadda kasuwar Kofar Wambai ita ma ta sha fama da makamanciyar irin wannan matsala.

%d bloggers like this: