✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnati ta rushe gidajen Musulmai sama da 300 a Indiya

Sai dai gwamnatin ta ce ta rushe gidajen ne sakamakon ginin da aka yi a filayen jama'a.

Sama da gidaje 300 na Musulmai ne gwamnatin Jihar Haryana ta kasar Indiya ta rushe a ranar Alhamis, sannan ta kama sama da mutum 150.

Mai magana da yawun jam’iyyar BJP mai mulkin Indiya, Raman Malik, ya shaida wa Al Jazeera cewa an yi rusau din ne domin a dakatar da gine-gine ba bisa ka’ida ba a filayen jama’a.

Rikicin ya fara ne bayan wata arangama da magoya bayan jam’iyyar BJP ta masu ra’ayin mazan jiya da reshenta na matasa, Bajrang Dal suka yi da wasu a gundumar Nuh ta Haryana, mai nisan kimanin kilomita 85 daga New Delhi.

Kungiyoyin biyu da ke da alaka da jam’iyyar BJP mai mulkin kasar, sun yi zanga-zangar tada tarzoma inda suka far wa mabiya addinin Musulunci da Kiristoci a Indiya.

Kungiyoyin Hindu sun zargi Musulmai – wadanda ke da kusan kaso 77 na mazaunan Nuh 280,000, bisa ga kididdigar da aka gudanar a 2011 – da haifar da tashin hankali.

Sun ce an jefe su da duwatsu tare da kone motocinsu, lamarin da ya haifar da rikici tsakanin al’ummomin biyu.

Musulmi sun ce abin da ya haddasa tashin hankalin shi ne wani faifan bidiyo a Facebook da wani fitaccen dan bangar Hindu, Monu Manesar ya fitar.

Sakamakon tashin tashinar da aka samu, an hana mabiya addinin cin naman shanu.

An haramta sayar da naman shanu a yawancin jihohin Indiya, yayin da aka dinga kashe mahauta, bayan hawan Fira Ministan Indiya, Narendra Modi, kan karagar mulki a 2014.

A Gurugram, wani birni mai yawan jama’a da ke bayan birnin New Delhi wanda, wasu gungun mutane sun yi wa wani limami dukan tsiya tare da caka masa wuka sannan suka kone masallacin shi.

An kai hari wani masallaci a Sohna, mai nisan kimanin kilomita 25 daga Gurugram.

An kashe mutane shida a rikicin a makon da ya gabata – ciki har da Musulmi da dan sanda mai gadin Sikh da kuma wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan Bajrang Dal ne.

Kazalika, kusan dukkanin gidaje da shagunan da aka kone na Musulmai ne.

A cikin ‘yan shekarun nan, jihohi da dama da ke karkashin jam’iyyar BJP, an lalata dukiyoyin Musulmin da ake zargi da shiga rikicin addini, ko kuma wasu laifuka.

%d bloggers like this: